Please wait…

 
Select a verse to play
Hausa - Saudi Qur'an Institute
Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce: "Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!" ﴾11﴿ To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa. ﴾12﴿ Kuma idan aka ce musu: "ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce: "Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani. ﴾13﴿ Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni,sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu,(3) sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne." ﴾14﴿ Allah Yana yin izgili(4) gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa. ﴾15﴿ Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba. ﴾16﴿ Misãlinsu(1) shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake għfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani. ﴾17﴿ Kurãme, bħbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa. ﴾18﴿ Ko kuwa kamar girgije mai zuba(2) daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kħwayewa ne gã kãfirai! ﴾19﴿ Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne. ﴾20﴿
Al-Baqara

وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا تُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ قَالُوا إِنَّمَا نَحْنُ مُصْلِحُونَ ﴿۱۱﴾ أَلَا إِنَّهُمْ هُمُ الْمُفْسِدُونَ وَلَٰكِنْ لَا يَشْعُرُونَ ﴿۱۲﴾ وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ آمِنُوا كَمَا آمَنَ النَّاسُ قَالُوا أَنُؤْمِنُ كَمَا آمَنَ السُّفَهَاءُ ۗ أَلَا إِنَّهُمْ هُمُ السُّفَهَاءُ وَلَٰكِنْ لَا يَعْلَمُونَ ﴿۱۳﴾ وَإِذَا لَقُوا الَّذِينَ آمَنُوا قَالُوا آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْا إِلَىٰ شَيَاطِينِهِمْ قَالُوا إِنَّا مَعَكُمْ إِنَّمَا نَحْنُ مُسْتَهْزِئُونَ ﴿۱۴﴾ اللَّهُ يَسْتَهْزِئُ بِهِمْ وَيَمُدُّهُمْ فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ ﴿۱۵﴾ أُولَٰئِكَ الَّذِينَ اشْتَرَوُا الضَّلَالَةَ بِالْهُدَىٰ فَمَا رَبِحَتْ تِجَارَتُهُمْ وَمَا كَانُوا مُهْتَدِينَ ﴿۱۶﴾ مَثَلُهُمْ كَمَثَلِ الَّذِي اسْتَوْقَدَ نَارًا فَلَمَّا أَضَاءَتْ مَا حَوْلَهُ ذَهَبَ اللَّهُ بِنُورِهِمْ وَتَرَكَهُمْ فِي ظُلُمَاتٍ لَا يُبْصِرُونَ ﴿۱۷﴾ صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لَا يَرْجِعُونَ ﴿۱۸﴾ أَوْ كَصَيِّبٍ مِنَ السَّمَاءِ فِيهِ ظُلُمَاتٌ وَرَعْدٌ وَبَرْقٌ يَجْعَلُونَ أَصَابِعَهُمْ فِي آذَانِهِمْ مِنَ الصَّوَاعِقِ حَذَرَ الْمَوْتِ ۚ وَاللَّهُ مُحِيطٌ بِالْكَافِرِينَ ﴿۱۹﴾ يَكَادُ الْبَرْقُ يَخْطَفُ أَبْصَارَهُمْ ےۖ كُلَّمَا أَضَاءَ لَهُمْ مَشَوْا فِيهِ وَإِذَا أَظْلَمَ عَلَيْهِمْ قَامُوا ۚ وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَذَهَبَ بِسَمْعِهِمْ وَأَبْصَارِهِمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ ﴿۲۰﴾